26 Disamba 2019 - 06:46
Iran Tana Maraba Da Duk Kokarin Magance Rikice-Rikice A Yankin

Shugaban majalisar tsare-tsare kan harkokin waje na kasar Iran, Dr. Kamal Kharrazi, ya bayyana cewar Iran tana nan a kan bakanta na zaman lafiya da kasashen yankin Gabas ta tsakiya, kamar yadda kuma take maraba da duk wani kokari na magance rikice-rikicen da ke faruwa a yankin.

(ABNA24.com) Shugaban majalisar tsare-tsare kan harkokin waje na kasar Iran, Dr. Kamal Kharrazi, ya bayyana cewar Iran tana nan a kan bakanta na zaman lafiya da kasashen yankin Gabas ta tsakiya, kamar yadda kuma take maraba da duk wani kokari na magance rikice-rikicen da ke faruwa a yankin.

Kamar Kharrazi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da jakadan kasar China a Iran Chang Hua inda yace sabani da rikice-rikicen da ake samu a yankin ya samo asali ne sakamakon dogaron da wasu kasashen yankin suka yi da kasashen yammaci musamman Amurka, yana mai cewa Iran ta yi amanna da cewa kasashen yankin ne za su iya magance rikice rikicen da ake fuskanta.

Har ila yau jami’in na Iran yayi ishara da jibge sojoji da Amurka take ci gaba da yi a yankin a matsayin daya daga cikin abubuwan da suke haifar da zaman dardar a yankin. Don haka yayi fatan alakar da ke tsakanin Iran da China za ta kara karfafuwa.

Shi ma a nasa bangaren jakadan kasar China ya ce kasarsa tana adawa da mulkin mallakar Amurka a duniya, kamar yadda kuma yace kasarsa tana goyon bayan aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da Iran ba tare da nuna wata wariya ba. 



/129